13 Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14 Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.
15 Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.
16 Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
17 Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.
18 Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.
19 Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza.