16 Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
17 Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.
18 Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.
19 Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza.
20 Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.
21 Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela.
22 Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza.