6 Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.
7 Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
8 Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.
9 Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan.
10 Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
11 Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.
12 Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel.