1 Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi.
2 Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra'ila da maganin hana ruɓa.
3 Suka ɗauki kwana arba'in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba'in.
4 Sa'ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir'auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir'auna, ku ce masa,
5 ‘Sa'ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan'ana.’ Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa'an nan in komo.”