12 Haka 'ya'yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta,
13 gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.
14 Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da 'yan'uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana'izar mahaifinsa.
15 Sa'ad da 'yan'uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.”
16 Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa,
17 ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.
18 'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”