1 Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata,
2 sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.
3 Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”
4 A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.
5 Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.