24 Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.
25 Sai ya ce, “La'ananne ne Kan'ana, bawan bayi zai zama ga 'yan'uwansa.”
26 Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan'ana kuwa ya bauta masa.
27 Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan'ana kuwa ya bauta masa.”
28 Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin.
29 Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.