3 Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.
4 Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato mushe.
5 Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa.
6 “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.
7 Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”
8 Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa.
9 “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku,