44 Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.
45 Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba.
46 A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa.
47 Dukan taron jama'ar Isra'ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa.
48 Idan baƙon da yake zaune tare da ku yana so ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji tare da ku, to, sai a yi wa kowane namiji da yake a gidansa kaciya sa'an nan ya iya shiga idin, shi kuma ya zama ɗan ƙasa. Daɗai, marar kaciya ba zai ci ba.
49 Wannan ka'ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.”
50 Isra'ilawa suka yi na'am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.