Fit 10 HAU

Fara

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu'ujizai nawa a tsakiyarsu,

2 domin kuma ka sanar da 'ya'yanka da jikokinka yadda na shashantar da Masarawa, na kuma aikata waɗannan mu'ujizai a tsakiyarsu. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.”

3 Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.

4 In kuwa ka ƙi yarda ka bar jama'ata su tafi, to, gobe zan aiko da fara cikin ƙasarka,

5 za ta rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za ta cinye sauran abin da ya kuɓuta daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a ƙasar.

6 Za su cika fādarka, da dukan gidajen fādawanka, da na dukan Masarawa. Iyayenka da kakanninka ba su taɓa ganin irin faran nan ba, tun daga ran da suke ƙasar, har wa yau.”’ Sai ya juya ya fita daga gaban Fir'auna.

7 Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”

8 Aka komar da Musa da Haruna gaban Fir'auna. Sai Fir'auna ya ce musu, “Ku tafi ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”

9 Musa ya amsa, “Da samarinmu, da tsofaffinmu za mu tafi, da 'ya'yanmu mata da maza za su fita tare da mu, da kuma garkunanmu da shanunmu, gama wajibi ne mu yi idi a gaban Ubangiji.

10 Fir'auna ya ce musu, “To, Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba, gama kuna da niyyar mugunta a zuciyarku.

11 Sai dai ku mazaje, ku tafi ku bauta wa Ubangiji, gama abin da kuke so ke nan.” To, aka kore su daga gaban Fir'auna.

12 Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa ƙasar Masar domin fara ta zo. Farar kuwa za ta rufe ƙasar Masar, ta cinye duk tsire-tsire da ganyayen da suke cikin ƙasar, da iyakar abin da ƙanƙara ta rage.”

13 Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.

14 Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.

15 Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.

16 Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

17 Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”

18 Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji.

19 Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.

20 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.

Duhu

21 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”

22 Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar.

23 Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune.

24 Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya ce musu, “Ku tafi ku bauta wa Ubangiji, sai dai ku bar tumakinku, da awakinku, da shanunku a nan, amma ku ku tafi da 'ya'yanku.”

25 Musa kuwa ya ce, “In haka ne, kai ka ba mu abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadayu da su.

26 Don haka sai mu tafi da dabbobinmu, ko kofato ba za a bari a baya ba, gama daga cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”

27 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna har bai yarda ya sake su ba.

28 Fir'auna ma ya ce wa Musa, “Tafi, ka ba ni wuri, ka mai da hankali fa, kada in ƙara ganinka, gama ran da na sāke ganinka ran nan kā mutu.”

29 Sai Musa ya amsa ya ce, “Haka nan ne kuwa, ba zan ƙara ganin fuskarka ba.”

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40