1 Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Faɗa wa Isra'ilawa su juya su yi zango a gaban Fi-hahirot tsakanin Migdol da bahar, a gaban Ba'alzefon. Sai ku yi zango gab da bahar.
3 Gama Fir'auna zai ce, ‘Aha, Isra'ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta cinye su.’
4 Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.