4 “Karusan Fir'auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar,Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
5 Rigyawa ta rufe su,Suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
6 Ya Ubangiji dantsen damanka, mai iko ne,Ya Ubangiji, dantsen damanka ya ragargaza magabta.
7 Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka,Ka cinye su kamar ciyawa.
8 Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru,Rigyawa ta tsaya kamar tudu,Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.
9 Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima,Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’
10 Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.