15 Sai Musa ya ce musu, “Ku shirya saboda rana ta uku, kada ku kusaci mace.”
16 A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.
17 Musa kuwa ya fito da jama'a daga zango ya shugabance su, su sadu da Allah, suka tsattsaya a gindin dutsen.
18 Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.
19 Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa.
20 Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.
21 Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama'ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu.