1 Sai wani mutum, Balawe, ya auro 'yar Lawi.
2 Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku.
3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.
4 Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.
5 Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.