2 Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.
3 Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari'a.
4 “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi.
5 Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.
6 “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari'a.
7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba.
8 Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya.