1 Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Faɗa wa Isra'ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa.
3 Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla,
4 da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya,
5 da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya,
6 da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa,