10 Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan.
11 Sa'an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya.
12 Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar.
13 Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar.
14 Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme.
15 “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye.
16 Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi.