1 “Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba'i.
2 A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.
3 Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.
4 Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa'an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.
5 Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.
6 Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla.