2 A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.
3 Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.
4 Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa'an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.
5 Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.
6 Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla.
7 Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.
8 Za ku yi bagaden da katakai, sa'an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.