2 A ɗinka wa Haruna ɗan'uwanka, tufafi masu tsarki domin daraja da kwarjini.
3 Ka kuma yi magana da gwanayen sana'a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina.
4 Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan'uwanka, Haruna, da 'ya'yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki.
5 Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
6 “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani.
7 Za a yi mata kafaɗa biyu, sa'an nan a haɗa su a karbunsu.
8 Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.