5 Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
6 “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani.
7 Za a yi mata kafaɗa biyu, sa'an nan a haɗa su a karbunsu.
8 Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.
9 A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai.
10 Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu.
11 Za a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu'ulu'u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya.