2 da abinci marar yisti, da waina wadda aka cuɗe da mai, wadda aka yi da garin alkama mai laushi.
3 Ka sa waɗannan abu cikin kwando, sa'an nan ka kawo su cikin kwandon, ka kuma kawo ɗan bijimin da raguna biyu ɗin.
4 “Ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwar ta sujada, ka yi musu wanka.
5 Sa'an nan ka kawo tufafin, ka sa wa Haruna zilaikar, da taguwar falmaran, da falmaran ɗin, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ka ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.
6 Za ka naɗa masa rawanin, sa'an nan ka ɗora kambi mai tsarki a bisa rawanin.
7 Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi.
8 “Sa'an nan ka kawo 'ya'yansa maza, ka sa musu zilaikun.