1 “Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya.
2 Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba'i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi.
3 Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya.
4 Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa.
5 Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.