2 Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba'i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi.
3 Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya.
4 Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa.
5 Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.
6 Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai.
7 Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun.
8 Zai kuma ƙona turaren sa'ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku.