35 Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke.
36 A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa'an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki.
37 Irin turaren nan da za ku yi, ba za ku yi wa kanku irinsa ba. Zai zama abu mai tsarki a gare ku, gama na Ubangiji ne.
38 Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama'arsa.”