22 Kowane katako an fiƙe bakinsa biyu don a harhaɗa su tare, haka ya yi da dukan katakan alfarwa.
23 Yadda ya yi da katakan alfarwa ke nan, ya kafa katakai ashirin a fuskar kudu.
24 Sai ya yi kwasfa arba'in da azurfa domin katakai ashirin. Kowane katako yana da kwasfa biyu saboda bakinsa biyu da aka fiƙe.
25 A fuska ta biyu ta wajen arewa ta alfarwa, ya kafa katakai ashirin.
26 Ya kuma yi kwasfa arba'in na azurfa. Kowane katako yana da kwasfa biyu.
27 Ya yi katakai shida a bayan alfarwa a fuskar yamma.
28 Ya kuma yi katakai biyu don kusurwar baya ta alfarwa.