1 Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba'i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.
2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla.
3 Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.
4 Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya.
5 Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna.
6 Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla.