4 Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya.
5 Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna.
6 Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla.
7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa'an nan ya robe cikinsa.
8 Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.
9 Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.
10 Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai.