13 A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
14 An zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi.
15 Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
16 Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
17 Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
18 Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba.
19 Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.