32 Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33 Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,
34 da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen,
35 da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa,
36 da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,
37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
38 da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar,