14 Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa.
15 Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.
16 Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi.
17 Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”
18 Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”
19 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.
20 Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.