28 Sa'an nan Musa ya faɗa wa Haruna abubuwan da Ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu'ujizan da ya umarce shi ya aikata.
29 Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra'ila.
30 Haruna dai ya hurta wa dattawan al'amuran da Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuma aikata mu'ujizan a idanunsu.
31 Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.