8 Ubangiji kuma ya ce, “Idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu'ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun.
9 Idan ba su gaskata mu'ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka ɗibi ruwa daga Kogin Nilu, ka zuba bisa busasshiyar ƙasa. Ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasa.”
10 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”
11 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne?
12 Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.”
13 Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.”
14 Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa.