1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,
2 “A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.
3 Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule.
4 Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.
5 Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa.
6 Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,