24 Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.
25 Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
26 Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen.
27 Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
28 Ya sa labule a ƙofar alfarwa.
29 Ya kuma sa bagade na ƙona hadaya a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da ta gari kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
30 Ya kuma sa daro a tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ya zuba ruwa a ciki don wanka.