20 Da suka fita daga gaban Fir'auna, sai suka sadu da Musa da Haruna, suna jiransu.
21 Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”
22 Sai Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangijina, me ya sa ka jawo wa wannan jama'a masifa? Me ya sa ka aike ni?
23 Gama tun da na tafi wurin Fir'auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama'a, kai kuwa ba ka ceci jama'arka ba ko kaɗan!”