1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, zan maishe ka kamar Allah ga Fir'auna. Ɗan'uwanka, Haruna kuwa, zai zama manzonka.
2 Kai za ka faɗa wa Haruna, ɗan'uwanka, dukan abin da na umarce ka, shi kuwa zai faɗa wa Fir'auna ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.
3 Amma zan taurare zuciyar Fir'auna don in aikata alamu da mu'ujizai cikin ƙasar Masar.
4 Amma Fir'auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama'ata, wato Isra'ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.
5 Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra'ilawa daga tsakiyarsu.”
6 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.
7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa'ad da suka yi magana da Fir'auna.