11 Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama'arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”
12 Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir'auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir'auna.
13 Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu.
14 Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi.
15 Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
16 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar.
17 Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa 'yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko'ina cikin ƙasar Masar.