1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, ka faɗa masa cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.
2 Amma idan ka ƙi sakinsu, wato kana ta riƙonsu,
3 to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani.
4 Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.
5 Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.”’
6 Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.
7 Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.