13 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.
14 A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama'arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya.
15 Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama'arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf.
16 Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.
17 Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba.
18 Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu.
19 Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.”’