15 Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama'arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf.
16 Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.
17 Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba.
18 Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu.
19 Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.”’
20 Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir'auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida.
21 Amma waɗanda ba su kula da abin da Ubangiji ya faɗa ba, suka bar bayinsu da dabbobinsu a waje cikin saura.