3 to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani.
4 Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.
5 Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.”’
6 Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.
7 Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.
8 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir'auna.
9 Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.”