1 Jawabin da annabi Habakuk ya hurta ke nan.
2 Ya Ubangiji, ina ta kukan neman taimako,Amma ka ƙi ji, sai yaushe za ka ji?Ina kuka a gare ka saboda zalunci,Amma ba ka yi taimako ba.
3 Me ya sa ka sa ni in ga mugunta,In kuma dubi wahala?Hallaka da zalunci suna a gabana.Jayayya da gardama sun tashi.
4 Ba a bin doka,Shari'a kuma ba ta aiki.Mugaye sun fi adalai yawa nesa,Don haka shari'a tana tafe a karkace.
5 Ubangiji ya ce,“Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani!Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki!Gama zan yi aiki a kwanakinka,Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
6 Ga shi, ina tā da Kaldiyawa,Al'umman nan mai zafi, mai fitina,Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya,Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.