11 Dutse zai yi kuka daga garu,Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.
12 “Tasa ta ƙare, shi wanda ya gina gari da jini,Ya kuma kafa birni da mugunta!
13 Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba?Sun kuma gajiyar da kansu a banza?
14 Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji,Kamar yadda ruwa ya cika teku.
15 “Taka ta ƙare, kai wanda yake sa maƙwabtanka su sha,Kana zuba musu dafinka har su bugu,Don ka dubi tsiraicinsu!
16 A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci.Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi.Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai faɗo a kanka,Kunya za ta rufe darajarka.
17 Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka,Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka,Saboda jinin mutanen da ka zubar,Da wulakancin da ka yi wa duniya,Da birane, da mazauna a cikinsu.