1 Addu'ar nasara wadda annabi Habakuk ya yi.
2 Ya Ubangiji, na ji labarinka,Sai tsoro ya kama ni.Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu,Ayyukan da ka saba yi.Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.
3 Daga Edom Allah ya zo,Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa.Ɗaukakarsa ta rufe sammai,Duniya kuwa ta cika da yabonsa.
4 Walƙiyarsa kamar hasken rana ce,Haske yana haskakawa daga gare shi,A nan ne ya lulluɓe ikonsa.
5 Annoba tana tafe a gabansa,Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.