12 Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.
13 Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.
14 Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka.
15 Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.
16 Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu?
17 Wannan shi ne wanda ya hallaka birane, ya mai da duniya hamada, wanda bai taɓa sakin ɗaurarru ko ya bar su su koma gida ba?”
18 Dukan sarakunan duniya suna kwance a cikin manya manyan kaburburansu,