1 Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce,“Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni,Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
2 Allah ne Mai Cetona,Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba.Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi,Shi ne Mai Cetona.”
3 Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki,Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.
4 A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce,“Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi!Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata!Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!
5 Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata.Bari dukan duniya ta ji labarin.
6 Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa!Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne,Yana zaune tare da mutanensa.”