1 Wannan shi ne jawabi a kan Mowab.Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa.
2 Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.
3 Mutane a tituna sun sa tsummoki a jikinsu, suka taru a filayen taruwa na birni da a kan rufin ɗakuna, sai makoki suke suna ta kuka.
4 Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai.
5 Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki.
6 Rafin Nimra ya ƙafe, ciyawar da take gefensa ta bushe, ba sauran wani ɗanyen abu.