1 Wannan shi ne jawabi a kan Masar.Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai.
2 Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko.
3 Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.
4 Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”