4 Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”
5 Ruwan Kogin Nilu zai ƙafe, a hankali kogin zai bushe.
6 Mazaunan kogin za su ji wari sa'ad da yake ƙafewa a hankali. Iwa da jema za su bushe.
7 Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su.
8 Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani.
9 Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya,
10 shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.